Ko da yake INEC tace ta kammala shirye-shiryenta na yin zabe, amma Majalisar Dattawa tace tana da rawar da zata taka, domin ganin cewa anyi zabe sahihi.
Saboda haka ne Sanata Kabiru Gaya ya bayyanawa Muryar Amurka cewa da zarar Majalisar ta fara zamanta, zai mika wani kuduri na musamman da zai dai-daita sahun duk wata shimfida da akayi na gudanar da zaben.
“Kasafin kudinta mun riga mun ware, tuni munce lallai kudin hukumar zaben nan, a bata kayanta.”
“Mataki ne wanda Allah Yake taimakon ‘yan Najeriya suke tsallakewa. Wannan gaskiya ne, wajibi ne zamu dauki mataki muna komawa Majalisa zamu kira kwamitin mu na hukumar zabe, da kwamitin kula da kudin Najeriya, sannan a kira ministan kudi, da shi Jega, a zaunar da su, a ji me ya faru. Wani mataki za’a dauka”, a cewar Sanatan daga Jihar Kano.
Sai dai, duk da wannan mataki da Majalisar Dattawa tace zata dauka, akwai barazana da ‘yan takara da manyan jami’ai ke fuskanta, da korafe-korafen kungiyoyi masu zaman kansu dake tuhumar gwamnatin Tarayya kan rashin daukan matakan da zasu kawo tsafta a tafiyar da wasu ayyukan gwamnati, harma da shimfida da hukumar zabe tace tayi kafin watan gobe.
Ranar 14 ga watan gobe, za’a fara zabe a Najeriya.