Jama’a da dama dai sun dade suna ta kiraye-kirayen gwamnatin Tarayya musamman saboda rashin samun katin zabe a Jihar ta Borno, lamarin da yasa wasu suka fara tunanin cewa ko gwamanti bata da niyyar gudanar da zabe a wannan Jiha.
Sai dai raba wannan kati ya kawo karshen wannan tunani da jama’a suke yi, amma mafi yawancin kananan hukumomi dake Jihar Borno, wadanda rikicin Boko Haram ya dai-daita, a cikin Kananan Hukumomin Maiduguri da Jere suke, wadda kuma hukumar zaben tabi sansaninsu, don raba wadannan katunan zabe ga irin wadannan al-umma.
“Mun samu damar baiwa mutane kusan 550” a cewar wani jami’in Hukumar Zabe.
Saboda korafe-korafe da wasu suke yi na cewa basu ga sunayensu ba, ga abunda jami’in zaben yace:
“Mutane suna kawo kuka, amma gwamnati ta samar da nau’rori wadanda ake amfani da su, ake sake musu rijista. Wanda bai samu nashi ba, yaje ayi masa sabo.”
Ranar 14 ga watan gobe, za’a fara zabe a Najeriya.