Cikin mutane 16,730 a yankuna shida na Abuja wadanda Institute of Human Virology ta yi gwaji cikin kwana hudu, don tunawa da ranar kanjamau ta duniya, mutane 190 kadai aka samu da cutar.
Yawan ya nuna raguwar yaduwar cutar a Abuja wanda kuma ya zama karon farko da ake samun kiyascin Abuja ya zama kasa da na kasa baki daya inji hukumar da tayi gwajin.
Masana na ganin raguwar masu dauke da cutar a matsayin abu mai farin ciki sai dai suna taka tsantsan da yada wannan labarin har sai an kamala tattara rahotonnin kasa baki daya inda ake sa ran gwada mutane a kalla 500,000.
A matsayin Abuja na daya daga cikin jihohi 13 da aka zaba don yaki da cutar kanjamau, “sai muyi taka tsan-tsan akan wannan ruhoton” inji Dr Eno Usoroh, ko’odinaton sashen Kanjamau, Zazzabin cizon sauro da tarin fuka na hukumar.
“Lokaci ya wuce da za’a rika kallon masu cutar kanjamau tamkar masu gobe da nisa. Har yanzu cutas ta zama cuta wadda bata warkewa domin har yanzu ba’a sami maganin da zai warkas da ita ba. Abin farin ciki ne ganin muna gwada mutane kuma da yawa daga cikinsu amsar su na nuna cewa basu da cutas” In ji shi.
“Wadansu daga cikin mutane 190 da amsar su ke nuna cewa suna dauke da cutar sun san matsayinsu tun kafin gwajin kuma suna so su tabbatas da matsayin su bayan sunyi imanin sun warke” inji ma’aikatan.
Wadanda aka yiwa gwajin sun hada da iyaye da ‘ya’yansu har da ‘yan shekara biyu da matasa da wadanda suke gwajin karo na farko kamar Abacha Danladi dan shekara 20 wanda yace yana amfani da kororon roba a koyaushe amma yana so a gwada shi, yace “ina kokari ne in kare kaina.”
Fitowar jama’a sosai a yankunan birnin tarayya kamar yankin Piwoyi, Pyakasa, Kabusa, Kucigoro ya nuna karuwar fahimta da karbuwar yanayin, a arewa ta tsakiya, inji shi.
Haka kuma yawan mata dake karbar yanayinsu dangane da cutar a Arewa ta Tsakiyar ya karu kadan daga kashi 17 cikin dari zuwa fiye da kashi 18 cikin dari, bias ga kididdigar da aka fitar a 2013 wanda hukumar kididdiga ta kasa ta gudanar.