A lokacin da take magana da manema labarai a ofishinta, mai kula da harkokin abinci ta jihar, Mrs Catharine Anger ta yaba wa yunkurin hukumar da ke kula da yara ta majalisar dinkin duniya wajen tallafawa shirin da kuma kungiyar Helen Keller da suka bayar da sinadarin Vitamin A. Sai dai ta koka cewa duk da wannan taimako, ba’a iya kaiwa ga wadansu yankuna musamman yankuna masu fama da tashin hankali ba.
Ta baiyyana cewa, tashin hankalin da Fulani suka haddasa sakamakon mamaye kananan hukumomin Agatu, Guma da Gwer-ta yamma a cikin jihar ya kara munana al’amarin, domin wadansu al’ummomi sun gudu daga kauyukansu hakan yasa ba’a iya kaiwa ga yaransu ba.
Yayinda wadansu da aka aika zuwa Agatu suka dawo domin tsoron matakan tsaron da aka sa a yankunan da ke fama da tashin hankali, Anger tace cikin kokarin kaiwa ga yaran, masu sanya ido sunyi tafiya har zuwa karamar hukumar Apa inda mutanen da suka rasa gidadensu ke samun mafaka.
Ta chigaba da baiyyana cewa a karamar hukumar Guma, sai da sojoji suka raka tawagar masu kula da kiwon lafiya zuwa masaukan wadanda suka gujewa gidajensu.
“Duk da yake babu tashin hankali a yanzu, bayanin tashin hankali na ci gaba da zama babbar barazana. Masu sanya ido sun sha wahala kaiwa ga kananan hukumomin Agatu da Guma. A zahiri saida sojoji suka raka tawagar masu kula da kiwon lafiya zuwa masaukan wadanda suka gujewa gidajensu.” “Ababen hawa sun zama wani kalubale na kaiwa ga mutanen da ya kamata akai gare su. Har yanzu akwai matsalar yaran da ba’a iya kaiwa gare su, a wasu yankuna masu wuyar shiga inda tashin hankula yafi kamari ba. Amma, baki daya za’a iya cewa an sami nasarar wannan shiri.” Inji Anger.