A lokacin da yake kaddamar da shirin karshe na wannan shekara na bayarda maganin rigakafin cutar ta shan inna mai gurguntawa ko kashe yara a Tureta, gwamnan na Sokoto yace kudurin gwamnatin jihar da dukkan wadanda wannan lamari ya shafa, shi ne ya kai ga samun irin wannan nasara.
Kwamishinan kiwon lafiya na Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu, wanda ya wakilci gwamnan, yace gwamnati ba zata yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da kawar da wannan cuta baki dayanta daga jihar. Yace an dauki matakai da daman a tabbatar da cewa an shawo kan masu kin karbar maganin.
Shi ma Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya roki dukkan sarakunan gargajiya da shugabannin addini da su tabbatar da cewa sun wayarda kan al’ummarsu game da bukatar yin wannan rigakafi.
Hakimin Bodinga, Alhaji Bello Abdul-Ra’uf shi ne ya wakilci Sultan na Sokoto a wannan taron.