Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwar Irma: Kusan Mutane miliyan Shida Aka Nemi Su Fice Daga Florida


Gwamnan jihar Florida, yayin da yake ba da umurni jama'a Florida su nemi mafaka
Gwamnan jihar Florida, yayin da yake ba da umurni jama'a Florida su nemi mafaka

A ranar Lahadin nan mai zuwa ake sa ran guguwar Irma za ta sauka a jihar Florida da ke Amurka, bayan da ta yi kaca-kaca da wasu yankunan Caribbea, inda har ta kashe mutane 22.

Yayin da guguwar Irma ke ci gaba da dumfarar jihar Florida da ke murka, hukumomi sun gargadi miliyoyin mutane da cewa su gaggauta ficewa domin lokaci na kurewa, a daidai lokacin da rahotanni ke cewa guguwar ta kashe mutane 22 a yankin Caribbea da ta fara ratsawa.

Akalla mutane miliyan biyar da 600 aka ba umurni su fice su nemi mafaka, wanda adadi ne da ya fi Quartan yawan al’umar jihar.

A ranar Lahadi aka yi hasashen guguwar ta Irma za ta kai ga jihar ta Florida.

Gwamnan jihar Rick Scott, ya kwatanta guguwar a matsayin “wani babban bala’i da jihar ba ta taba gani ba, inda ya kara da cewa fadin guguwar ya fi fadin jihar.

Gwamna Scott ya kara jaddada cewa, lokaci na kurewa, domin kusan za a iya cewa guguwar ta riga ta iso.

Hasashen baya-bayan nan da aka yi, ya nuna cewa, idon guguwar ya dan karkata daga sauka kai tsaye a yammacin jihar ta Florida, hakan kuma na nufin tsakiyar birnin Miami, wanda ke dauke da mutane miliyan shida, ba zai shafu sosai ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG