Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kera Na'urar Robot Da Zata Iya Zuwa Cefane


Wani kamfanin da ya shahara wajen kirkirar na'ura mai sarrafa kanta (Robot) don taimakawa jama’a gudanar da ayyukan yau da kullun, ya fadada aikin da na'urar da suke kirkira zata dinga yi.

Kamfanin Starship tare da hadin gwiwar kamfanin Co-op Milton, sun kammala kirkirar wanta na'ura da zata zama 'yar aike, wadda za ta iyimwa mutane cefane, ko sayo abinci a gidajen sayar da abinci.

Masana na ganin wannan tsarin zai dauki lokaci mai tsawo kamun wadannan na'urorin su zama jiki, mutane su saba da su da amincewa da irin ayyukan su.

Robot din na tafiya cikin saurin da ya kai nisan kilomita 16.1 cikin awa daya, kuma zai iya shiga cikin taron jama’a don isar da sako batare da ya bace ba. Kamfanin zai wadatar da wannan na'urar a cikin birnin Landon daga nan zuwa shekarar 2019.

Robot din kuma na dauke da kyamara guda hudu da na'urar GPS don gane idan akwai wata matsala a hanya don canzawa idan bukatar hakan tazo, jim kadan kamun ya isa gidan mutun za'a aika ma mutun sakon gaggawa da cewar dan aiken shi na kan hayyar isowa cikin 'yan mintoci, don a sa ido.

Kamfanin kuma ya tabbatar da cewar har ya zuwa yanzu babu wani abu da ya taba samun wanna na'urar, ko a hanya ko kuma bayan isar da sako a gidajen jama’a.

Za’a fara gwajin wanna na'urar a cikin jami’o’in dake cikin birnin Landon, Amurka da Jamus a cewar mai magana da yawun kamfanin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG