Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yariman Saudiyya Sultan Bin Salman Ya Biya Sadakin $50 Milliyan


Ana zargin Yarima Sultan Bin Salman, na kasar Saudi Arebiya, da biyan makudan kudade a matsayin sadaki na wata mata da ya aura mai shekaru 25, kudin da suka kai dallar Amurka milliyan hamsin $50, kwatankwacin naira billiyan goma sha takwas N18B.

Amaryar ‘yar asalin yankin kasashen larabwa wadda ta karbi manya manya kyaututtuka, baya ga kudin sadakin ta na dallar Amurka $50M, an gudanar da shagulgulan bukin a katafaren otel din “Four Season” dake makociyar kasar Saudiyya kasar Kuwait.

Yariman mai shekaru 68, wanda ya auri matashiya mai shekaru 25, auren dai ya ja hankalin jama’ar yankin, wanda aka hada jerin motoci kirar Range Rover sama da ashirin wajen daukar amarya da kayan gara.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG