Wani sabon rahoton hukumar dake kula da hanyoyin sadarwa ta Majalisar Dinkin Duniya, International Telecommunication Union, yace kashi ‘daya cikin hudu na mutanen duniya masu amfani da yanar gizo matasa ne da shekarunsu suka fara daga 15 zuwa 24.
Rohotan ITU ya kara da cewa kusan kaso 40 cikin 100 na mutanen dake amfani da yanar gizo a duniya, kimanin mutane miliyan 320 sun fito ne daga kasashen China da Indiya.
A baya dai China ta ce akwai masu amfani da yanar gizo sama da miliyan 730 a kasar. Wanda hakan ya ninka yawan masu amfani da yanar gizo a Amurka, inda akwai kusan mutane miliyan 287. Sai dai kuma rahotan ya gano cewa matan dake amfani da internet sunfi maza yawa a Amurka.
A daya bangaren kuma, Indiya ta wuce tsammanin manazarta, domin kuwa akwai mutane miliyan 460 dake amfani da internet a kasar.
Haka kuma rahotan ITU ya gano cewa akwai banbancin jinsi, inda maza suka fi yawan matan dake amfani da internet a duniya da kaso 12 cikin 100. Wanda hakan ya banbanta a kasar Amurka inda yawan matan ya wuce na maza da kaso 3 cikin 100.
Fasahar intanet fasaha ce da wasu masana ke cewa ta sauya fasalin yadda ake gudanar al'amuran rayuwa a duniya gaba daya, har ta kai wasu na cewa sun fara mantawa da ko yaya rayuwa take kafin zuwan Intanet.
Facebook Forum