Kamfanin wayoyin Apple sun shirya tsaf, don tunkarar duniyar kimmiya da fasaha, wanda sabuwar wayar su take dauke da wani sabon tsari da ake kira ‘Augmented Reality’ tsarin da suka saka a cikin sabuwar wayar su da zasu kaddamar nan bada jimawa ba.
Yadda tsarin ke aiki shine, mutun zai dinga ganin gilashin wayar shi kamar yadda zaiga abu a hannun shi, idan mutun na kallon hoto, ko bidiyo a wayar zai dinga ganin rubu kamar a tafin hannun shi.
Wannan sabon tsarin kamfanin Apple, su zasu fara amfani da shi a duniyar kimmiya. Kamfanin sun shirya sosai, don su kara yawan kudaden shigar su, tun bayan mutuwar shugaban kamfanin Mr. Steven Jobs, kamfanin ya fuskanci koma baya a kudaden shiga.
Amma wannan sabon tsarin da suke son fitarwa a kasuwa, zai iya taimakawa wajen kara samun kudaden shiga ga kamfanin, kana da kara wayar da kan duniya akan harakar ilimin zamani.
Ita dai sabuwar wayar za tazo da wasu sababbin abubu wanda sai wanda idon shi ya kai, duk wanda ya taba buga wasan bidiyo game na “Pokemon Go” zai iya samun burbushin yadda sabuwar wayar take.
Facebook Forum