Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gomman Mutane Sun Mutu A Sabon Harin Da Aka Kai Mali

Shugaban rundunar sojin Mali, Oumar Diarra a Bamako
Shugaban rundunar sojin Mali, Oumar Diarra a Bamako

Kwararrun sun ce, hare-haren na ranar Talata a Bamako, su ne irinsu na farko cikin shekaru da dama, kuma sun yi mummunar illa ga gwamnatin mulkin soja da ke mulki a kasar.

Wani harin da aka kai a Bamako, babban birnin kasar Mali, wanda aka auna sansanin horar da ‘yan sanda sojoji da filin jirigin sama, ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 70 tare da jikkata wasu 200, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana a ranar Alhamis.

Wannan shi ne hari mafi muni na adadin mutanen da suka mutu a ‘yan shekarun baya bayan nan.

Kwararrun sun ce, hare-haren na ranar Talata a Bamako, su ne irinsu na farko cikin shekaru da dama, kuma sun yi mummunar illa ga gwamnatin mulkin soja da ke mulki a kasar.

Adadin wadanda suka mutu ya sanya shakku kan dabarun gwamnatin mulkin soja da suke yi na cewa an shawo kan matsalar tsaro duk da cewa ‘yan bindiga sun shafe shekarun suna yawo a yankin.

Harin da kungiyar al-Qa’ida da ke da alaka da kungiyar JNIM ta yi ikirarin kai wa ya haifar da kaduwa da tofin Allah tsine a cikin wannan kasa ta yammacin Afirka.

‘Yan kasar ta Mali da dama sun yi amfani da shafukan sada zumunta wajen nuna gazawar jami’an tsaro.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG