Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Anambra Ta Kafa Kwamiti Kan Gobarar Da Ta Lakume Shaguna A Kasuwar Nkpor


Hotunan Baya Baya: Gobarar Kasuwa A Jihar Borno
Hotunan Baya Baya: Gobarar Kasuwa A Jihar Borno

Gwamnatin jihar Anambra ta kafa wani kwamitin bincike don gano ainihin musabbabin gobarar da ta lakume shaguna da dama a kasuwar Nkpor da ke kusa da garin Onitsha, yayin da wadanda al’amarin ya shafa na ci gaba da kirga asarar da suka tafka.

Kakakin gwamnatin jihar, Christian Aburime, ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da Sashen Hausa na Muryar Amurka jiya Lahadi, inda ya kamanta al’amarin da babbar asara.

Aburime ya kara da cewa, “Gwamnati ta ga al’amarin, kuma za ta binciki duk abin da ya faru, don tabbatar da hakan bai sake faruwa ba.”

Chinedu Nwokocha wani kwararre ne akan tsaron jama’a, kuma ya bayyana abin da ya kamata a yi don magance matsalar tashin gobara a kasuwanni.

Ya ce, “Yana da muhimmaci a tsara wani shiri don fadakar da jama’a game da aukuwar gobara a kasuwanni, kuma ya kamata a samu tsarin gaggawa na ceton rayuka da dukiyoyi. Za a yi ne da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, watau da gwamnati da Hukumar Kashe Gobara da ‘yan kasuwa, da kuma kwararru.”

Chinedu ya kuma bukaci a horas da masu aikin agaji daga cikin ‘yan kasuwa da masu gadin kasuwa kan yadda ake kashe gobara, tare da gina wuraren tara ruwa a kowace kasuwa.

A cikin wannan makon da ya gabata ne aka samu barkewar gobara a kasuwar garin Nkpor, inda sama da shaguna talatin suka kone kurmus, ciki har da shagon Shugaban Kungiyar Kasuwar, Paul Okafor, wanda ya ce an rasa kayayyakin da suka kai kimanin nera miliyan 300.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG