Dan majalisar dattawa mai wakiltar kudancin jihar Borno, Ali Ndume, yayi na'am, da ummarnin da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bada ne cewa hedkwatar rundunar Sojojin kasar ta koma Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
A wata hira da ya yi da Haruna Dauda, wakilin Muryar Amurka Yace yunkurin shugaban kasa abun yabo ne domin abun da suke fata ne suna kuma jira-inji Ali Ndume.
Girke manyan dakarun tsaro a Maiduguri zai taimaka matuka. Yin hakan zai kawo karshen tashin tashinar 'yan Boko Haram. Yace dama can matsalar ita ce masu yaki suna wuri daban masu bada umurni kuma suna wani wuri daban. Ya kwatanta lamarin da mara lafiya da likita. Idan mara lafiya da likita basa wuri daya ba za'a samu warkewa ba.
Dangane da cewa Sanata Ndume ya janye daga neman shugabancin majalisar dattawa domin wai shugaban kasa yana goyon bayan wani sai yace babu gaskiya a maganar. Yana neman kujerar kuma shugaban kasa bai goyi bayan kowa ba. Yace idan jam'iyya ta tsayarda shawara akan inda shugaban majalisar zai fito zasu bi umurnin.