Ibrahim Alfa Ahmed
Washington, DC - Matasa su fiye da dubu daya ne dake shugabancin kamfanoni dabam-dabam a ciki da wajen Najeriya zasu hallara a Abuja domin gudanar da wani taron koli da kuma baje kayayyaki a ranakun 3 da 4 ga watan Agusta.
Shugaban wata kungiyar matasa kwararru da ake kira "Nigerian Young Professionals Forum", Moses Siasia, yace za a gudanar da taron ne a Cibiyar Taro ta Rundunar Mayakan Saman Najeriya.
Siasia ya ce taron "zai ba matasa masu hazikancin kasuwanci a fadin Najeriya damar musanyar ra'ayi da takwarorinsu daga kowane lungu na duniya."
Yace taron zai maida hankali kan kanana da matsakaitan masana'antu da kamfanoni, tare da ba wadanda zasu halarta damar kulla hulda sauran 'yan kasuwa na Najeriya da na Afirka.
Taron zai maida hankali kan muhimman bangarorin tattalin arziki kama daga Noma, Man Fetur da Gas, Hanyoyin Sadarwar Zamani, Masana'antu da sauransu.