Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Kalubalen Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari da John Kerry na Amurka
Shugaba Muhammadu Buhari da John Kerry na Amurka

Baya ga matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, batun karancin wutar Lantarki da rashin aikin yi a tsakanin matasa, na daya daga cikin manyan kalubalen Gwamnati shugaba Muhammadu Buhari, a Najeriya.

A baya dai gwamnati Goodluck Jonathan, ta sayarda tashoshin wutar Lantarki ga wasu kamfanoni masu zaman kansu da nufi shayo kan matsalar wutar Lantarki a kasar.

Amma daga dukkan alamu haka bata cimma ruwa ba, al’amarin da wasu ke ganin maida tashoshin samarda wutan Lantarki hannu Gwamnati shine mafi a’ala.

Amma a nasu gefen ‘yan kasuwar da tashoshin samarda wutar Lantarkin ke hannunsu sun bayana inda matsalar take, kanal Sani Bello mai retaya shugaban Mainstream Energy Solution, dake kula da tashoshin Kainji da Jebba yace inda kamfaninsu na samarda wutar Lantarki amma an hanasu sa shi a layin wuta domin yana iya kashe layin domin layin ya tsufa.

Ya kuma kara da cewa layukan wutar har yanzu Gwamnati bata inganta shi bata kuma baiwa ‘yan kasuwa ba balle su ingataci idan hakkan bai samu ba kome akayi wahala ce kawai.

XS
SM
MD
LG