Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taba Sigari na Kai Mashayinta Kabari Kusa


Shan Taba Sigari
Shan Taba Sigari

Yau itace ranar da hukumar lafia ta duniya, ta ware don wayar da kan al’umah, a kan illolin shantaba sigari, ga lafiya dan’adam. Jami’an kiwon lafiya a matakai daban-daban na amfani da wannan ranar don kara wayar da kan al’uma.

A zantawa da wakilinmu Nasiru Batsari, yayi da Dr. Usman Muhammad, wanda ya kara bayyanar da ilolin shan taba ga duk mahaluki, inda yake nuni da cewar ita wannan tabar tana lalata huhun dan’adam dama wasu sassan jikin, kuma tana haifar da cututuka masu tsawon illa ga jikin bil’adam. Don haka yakamata jama’a su guji wannan busa hayakin da kan kaisu ga halaka.

Malam Ahmad Abdullahi Tela, wani tsohon mashayin sigari yayi nuni da irin ilolin da taba kan haifar idan mutun yana shan tabar a kowane irin hali. Wanda kuma ya nuna irin ban-bancin da yagani tsakanin lokacin da yake shan tabar da ya barin a yanzu. Yanzu haka dai yana ganin cewar duk wanda ke shan taba to lallai yana kashe kanshi ne kawai da kanshi. Don haka yakamata mutane su yima kansu kiyamun laili wajen tafiyar da rayuwarsu.


  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG