Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Kashe Akalla Mutane 11


Wata girgizar kasa mai karfi aji 5.9 ta abkawa yankin Arewa maso yammacin kasar Haiti a jiya Asabar, inda ta kashe akalla mutane 11 da raunata wasu fiye da 130.

Wani kakakin gwamantin kasar ya gayawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa akalla mutane 7 suka mutu a Port de Paix babban birnin yankin. Wasu mutane 4 kuma suka mutu a garin Gros Morne mai tazarar kilomita 50 daga binin na Port de Paix.

An samu labarin cewa gidaje da asibitoci sun ruguje sanadiyar wannan girgizar kasa. Hukumar Haiti mai kulla da bada agajin gagawa tace "garin Port de Paix, Gros-Morns, Chansolme tare da Tortuga sune wadanda suka fi fuskanta matsalar.

Ofishin gwamantin Amurka mai kula da yanayi yace wannan karamin girgizar kasar, mai karfi maki 5.9 ya kai zuwa kilomita 19 daga babban birnin Port de Paix dake Arewacin tekun kasar.

Shugaban kasar ta Haiti, Jovenel Moise ya shawarci al’ummar kasar da su kwantarda hankalinsu. Ya kara da cewa, gwamantin kasar zata maida hankalinta wajen taimakawa wadanda bala'in ya shafa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG