Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Melaniya Trump ta Isa Masar


Melania Trump a Masar
Melania Trump a Masar

A ziyarar kasashe hudu da uwargidar Shugaban Amurka Melaniya Trump ta ke yi, ta isa kasa ta hudu kuma ta karshe wato Masar, inda aka ma ta kyakyawar tarba, kamar yadda aka ma ta a kasashen Ghana da Malawi da kuma Kenya.

Uwargidar Shugaban Amurka Melania Trump ta isa birnin Alkhahira na kasar Masar Jiya Asabar, inda Shugaba Abdel Fattah al-Sisi da matarsa, Entissar, su ka marabceta da wata liyafa.

Bayan ziyarar fadar Shugaban kasa da kuma Ofishin Jakadancin Amurka da ke binrin Alkhahira, Melania Trump za ta ziyarci gine-ginen dalar sarakunan Masar na zamanin da da kuma babban umudin Giza.

Masar ce ta karshe cikin kasashen Afirka hudu da Melania Trump ke ziyara.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG