Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Zargi China Da Yi Mata Zagon Kasa


Gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Donald Trump na zargin China da yinkurin yi mata zagon kasa, ta wajen shiga sharo ba shanu a tsarin siyasar Amurka.

A wani jawabi jiya Alhamis, Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence ya ce, "China so ta ke wani dabam ya zama Shugaban Amurka," ya na mai zargin China da abin da ya kira, "katsalandan a tsarin dimokaradiyyar Amurka" ta wajen amfani da tasirinta ta hanyar da ba ta kamata ba.

Wadannan kalaman na zuwa ne mako guda bayan da Shugaba Trump ya zargi Chinar da yinkurin yin katsalandan a zaben Amurka na rabin wa'adi wanda za a yi a watan gobe, kuma Shugaba Trump ya ce Mr. Pence zai gabatar da cikakken shaida daga bisani.

Mr. Pence ya zargi Jam'iyyar 'Yan Gurguzu wadda ke mulkin China da abin da ya kira, "biya ko tilasta wasu 'yan kasuwa, da masu hada fina-finai, da jami'o'i, da kwararru, da malaman jami'o'i, da 'yan jarida, da jami'an gwamnatin jahohi da na tarayya. Uwa-uba, China ta dau matakin da ba ta taba yi ba na sauya ra'ayoyin Amurkawa, da zaben 2018, da kuma yanayin kasar da zarar an doshi zaben shugaban kasa na 2020."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG