Ana amfani da harshe wajen hada al’ummomi, da bada gudummuwa ga ci gaba, da karfafa zaman lafiya da tsaro. Kafofin watsa labarai na amfani da fassara wajen yada wadannan manufofin, musamman a wannan lokaci da duniya ta dunkule ta zama daya.
Taken bukin wannan shekarar shi ne, “Duniyar Da Babu Shinge”, wato duniyar da bambance-bambancen harshe basu zama shamaki ga ci gaban al’ummomi ba.
Tabbas Juya sako daga wani harshe zuwa wani muhimmin abu ne a mu'amullar jama'a da kuma sadarwar kafofin watsa labarai, shi ya sa masu wannan aikin suke da muhimmanci, kamar yadda tsohon Editan Muryar Jamus da sashen Hausa na gidan rediyon Ghana (GBC), Sarki Jibril Sissy ya bayyana.
Ya kuma ce ba haka kawai Majalisar Dinkin Duniya ta kebe wannan rana domin karrama wadanda suke harkar fassara ba saboda gudummuwar da suke bayarwa wajen hadin kai, ci gaba da tsaro a duniya.
Abdallah Sham’un Bako, wakilin sashen Hausa na gidan rediyon RFI a Ghana, ya jaddada muhimmancin masu fassara domin isar da bayanai ga jama’a da suke yi. Yace, fassara na da wahala sosai musamman ga masu isar da sako ga al’ummar da ba sa amfani da Hausa.
Kamar yadda kwararru suka ce, sadarwa bata kammaluwa sai dayan bangaren ya fahimci abinda ake nufi. Hakan ya sa jami’un yada labarai da harshen Hausa a Ghana suke fuskantar kalubale, in ji Maryam Bawa ta gidan rediyon Marhaba.
Sabili da mulkin mallaka yawancin kasashen Afirka na magana da harshen kasashen da suka mallakesu a hukumance. Ingilishi ne harshen da hukumomin Ghana suke amfani da shi don isar da sako ga jama’a. A saboda haka, tilas ne jami’un watsa labarai da harshen Hausa su yi taka-tsan-tsan wajen fassara sako ga jama’a a harshen.
Sarki Jibril sissy ya shawarci ‘yan jarida da su inganta fassararsu ta hanyar samun horo da cudanya da mutanen da ake fassarar zuwa ga harshensu, da karance-karance a kan wannan harshen domin kara kwarewa sosai.
Akwai harsuna kimanin 6,000 a duniya, 2,000 a Afrika suke kuma mutane kimanin biliyan 1.21 ne suke magana da wadannan harsunan.
Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah: