Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Dimokradiya Ta Duniya


Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Anthony Guterres
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Anthony Guterres

A shekara ta 2007, babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya ayyana ranar 15 ga Satumba a matsayin ranar dimokradiyya ta duniya. Tun daga wannan lokacin, ranar ta zama wata dama ta shekara ta duba matsayin dimokradiyya a duniya.

ACCRA, GHANA - A jawabinsa na ranar ta shekarar 2022, babban sakataren majalisar dinkin duniya António Guterres ya bayyana cewa ma'aikatan yada labarai suna fuskantar takunkumi, cin zarafi, ana kullesu, har ma da kisa, galibi ba tare da hukunci ba. Irin wannan duhun tafarkin babu makawa yana haifar da rashin zaman lafiya, rashin adalci da fiye da haka.

Ya ci gaba da cewa, Idan babu ‘yancin ‘yan jarida, dimokradiyya ba za ta iya rayuwa ba. Idan babu ‘yancin fadin albarkacin baki, babu ‘yanci. A ranar Dimokradiyya da kowace rana, bari mu hada karfi da karfe don tabbatar da 'yanci da kare hakkin kowa da kowa, a ko'ina.

Bikin ranar dimokradiya na wannan shekarar shi ne karo na 15 kuma ya mayar da hankali ne kan muhimmancin ‘yancin yada labarai ga dimokradiyya, zaman lafiya, da isar da manufofin ci gaba mai dorewa.

Da ya ke bayani a kan muhimmancin wannan ranar da kuma taken wannan shekarar, Zakariya Tanko, Malami a jami’ar koyar da aikin jarida na Ghana (GIJ), yace lallai tun da yake al’umma ce ta zabi shugabanni su jagorancesu to ya kamata su san ababan da ke tafiya, kuma ‘yan jarida ne suke sanar da su hakan. A saboda haka, ‘yancin yada labarai na da muhimmanci ga dimikradiya.

Wasu ma’aikatan yada labarai a Ghana sun bayyana wa Muryar Amurka ra’ayinsu game da yadda dimokradiyar Ghana ta ba su damar gudanar da aikinsu da kuma kalubalen da suke fuskanta.

AbdulHanan Adam na gidan telebijin na GHO, yace dimokradiya ta ci gaba a Ghana sai dai ‘yan jarida suna fuskantar kalubale. Ya bada misali da wasu ‘yan jarida da aka ci zarafinsu, har wani ya rasa ransa domin rahotanni da suka fitar.

A nasa bangaren Salihu Shu’aibu Sarauta, ya nuna cewa a dunkule ‘yan jarida sun samu ‘yancin gudanar da aikinsu a Ghana, duk da cewa akwai wasu kalubale da ba za a rasa ba.

A karshe Issah Mairago Jibril Abbas, dan jarida kuma mai fashin baki akan al’amuran yau da kullum ya shawarci gwamnati da ta daina muzgunawa kafofin yada labarai.

Kafofin yada labarai masu 'yanci, masu zaman kansu, masu sanar da jama'a al'amuran da suka shafe su, muhimmin abubuwa ne ga dimokradiyya. Suna bai wa jama'a damar yanke shawara mai kyau da kuma sa gwamnatoci yin taka-tsan-tsan wajen gudanar da harkokinsu.

Saurari rahoton Idris Abdallah Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:07 0:00
XS
SM
MD
LG