Ranar hausa ta duniya wace ta sami asali daga shawarar da wani mai amfani da Twitter ya bayar yau shekaru a kalla 8, inda ya nemi Majalisar Dinkin Duniya ta sanya ta a jerin ranakunta, sannan da ya bukaci masu jin harshen Hausa dake amfani da wannan kafar sadarwa su maida hankali wajen rubuce rubucensu da Hausa domin yada al’adun Hausa ta yadda duniya za ta kara fahimtar wannan yare da ya zama hanyar sadarwar miliyoyin mutanen dake zaune a kasashen Afrika ta tsakiya da na yankin yammacin Afrika cikinsu har da Jamhuriyar Nijer.
Domin karrama wannan rana, kungiyar marubuta a harsunan Nijer wato ASAUNIL ta shirya bukin baje koli da zai gudana a masarautar Sultan na Damagaram akamar yadda sakatariyar yada labaran wannan kungiya Hajiya Halima Djido ta bayyana a hirar ta da Muryar Amurka.
A wani hadin guiwa da hukumomin ilimi kwamitin tsare tsaren hidimomin ranar hausa ya shirya mahawwarar bainar jam’a akan tarihi da al’adun malan bahaushe tare da baje kolin samfarin tufafin al’ummar Hausa dukkansu a yau juma’a a gidan kallo da ajiyar kayan tarihi Musee Nationale Boubou Hama dake Yamai.
A ci gaban wadanan shagulgula kungiyar ASUNIL ta ware lokaci na musamman domin karrama wasu fitattun ma’aikata da lambobin yabo galibinsu 'yan jaridar kasa da kasa saboda gudunmuwar da suka bayar wajen bunkasa harshen Hausa a duniya.
Bincike ya yi nuni da cewa a yau harshen Hausa na daga cikin mafi mahimmanci a kasashen Najeriya , Nijer, Kamaru, Tchad, Soudan, Ghana, Togo, Jamhuriyar Benin, da Gabon.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: