Kwana kwanan nan Abubakar Shekau ya yi jawabi kamar yadda ya saba yi yana cewa har yanzu yana kan mukaminsa ya kuma yiwa gwamnati tsageranci de cewa zai cigaba da abubuwan da yake yi. To kashe-kashe musamman a jihar Borno sai karuwa suke yi. Ranar lahadin nan da ta wuce mutane fiye da hamsin suka rasa rayukansu gap da suka gama salla. Boko Haram itace ta bindigesu har lahira. To ko menene ya sa hakan na cigaba da faruwa musamman a jihar Borno duk da dokar ta baci da aka kakaba mata?
Domin samun ansa ga wannan tambayar abokin aiki Sahabo Aliyu Imama ya zanta da Alhaji Nuhu Aliyu tsohon matamakin sifeton 'yansandan Najeriya. Ya ce yadda gwamnati ta dauki matakan tsaro da aiwatar da dokar ta baci a ce kuma har yanzu ana kashe-kashe akwai damuwa akwai kuma tsoro. Yakamata jami'an tsaro da aka dora ma hakin kawo zaman lafiya su hada kansu su sake yin nazari domin su san yadda zasu fito ma lamarin.
Kodayake da wuya a ce jami'an tsaro na koina a jihar Borno to amma idan 'yan ta'adan sun koma suna barna a kauyuka da kewayen gari kamata ya yi gwamnati ta bankado duk inda suke. Su yi nazarin yaya yakamata su tashi tsaye su fuskanci 'yan ta'adan. Ya ce shi yayi imani gwamnati tafi karfinsu amma ya ce da alama 'yan ta'adan sun fi bada ransu ga ta'adancin da suke yi fiye da yadda jami'an tsaron kasar suka bada ransu ga aikinsu. Wato 'yan ta'ada suna yin abinsu ne da zuciya daya yayin da jami'an gwamnati na yin aikinsu da zuciya biyu. Ya kamata jami'an gwamnati su ma su jaje. Duk abin da yakamata gwamnati ta yi masu ta yi domin su ma su sadakar da rayukansu. Ya ce abun nada ban kunya. Ya ce ta yaya za'a ce jami'an gwamnati da suka yi karatu suka samu horo kuma suna samun albashi a ce wadanda basu da karatu ko horo ko albashi sun fisu jajewa. Abun na bada kunya. Ya kamata asake lale domin bisa ga alamu da walakin a harkikin jamai'an tsaron kasar Najeriya
Ga karin bayani.