A yayin da ake cigaba da shirye shiryen fara gasar cin kofin kwallon Kafa ta duniya a wannan shekara ta 2018, a can kasar Rasha, gobe hukumar dake kula da wasan kwallon Kafa ta duniya Fifa ta bayyana sunan Nestor Pitana, a matsayin alkalin wasan da zai hura a wasan farko na bude gasar gobe tsakanin masu karbar baki wato kasar Rasha, da takwararta ta kasar Saudi Arabia, a birnin Moscow Luzhniki.
Nestor mai shekaru 42 da haihuwa yana daya daga cikin alkalan wasan da suka hura wasa a yayin wasan cin kofin duniya da ya gabata a shekarar 2014 a kasar Brazil.
Alkalin wasa Nestor Pitana, zai samu taimako daga alkalan wasa na gefe wadanda suka hada da Juan Pablo Bellati, da Hernan Maidana, sai kuma Sandro Ricci daga kasar Brazil a matsayin Mataimakin alkalin wasa na hudu a yayin wasan gobe wanda zai wakana da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi.
Facebook Forum