Shugaban gwamnatin rikon kwarya, Bah N’Daw, wanda kwamitin sojojin da ke mulkin kasar suka nada ranar Juma’ar da ta gabata ne ya nada Ouane a matsayin Firai Minista a jiya Lahadi yayin da shi kuma wanda ya jagoranci juyin mulkin, Kanal Assimi Goita ya zama mataimakin Shugaban kasa.
Ouane, ya yi aiki a matsayin ministan harkokin waje daga shekarar 2004 zuwa 2011, bayan da ya wakilci Mali a matsayin jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya daga shekarar 1995 zuwa shekarar 2002.
Ta yiwu nadin Ouane a matsayin Firayim Minista ya kai ga janye takunkumin da kungiyar kasashen ECOWAS ta kakaba wa Mali bayan da dakarun sojin kasar suka kama Keita dan shekaru 75, da kuma Firayim Ministan sa a lokacin Boubou Cisse a ranar 18 ga watan Agusta a gidan Keita da ke Bamako babban birnin kasar.
Facebook Forum