Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Libya Ta Maido Da Ayyukan Hakar Man Fetur


Wani filin ayyukan hacker ma a Libya, 2014.
Wani filin ayyukan hacker ma a Libya, 2014.

Rahotanni daga Libya na cewa, an dawo da ayyukan hakar mai a wasu wurare biyar da ke kasar, bayan da aka kwashe wata takwas ba a gudanar da ayyukan.

Daga cikin wuraren hakar man da aka koma aiki, har da babbar tashar Al – Sharara wacce ta fi kowacce girma a kasar.

Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa an dan samu tashe-tashen hankula a nan da can a Tripoli babban birnin kasar ta Libya, amma kuma batun maido da ayyukan hakar man, ya mamaye matsalar tsaron da ake fuskanta.

Shugaban dakarun da ke tsaron tashoshin man fetur din kasar Janar Naji Maghrebi, ya fadawa kafofin yada labaran kasasashen larabawa cewa, an maido da ayyukan hakar mai a tashoshin Zoueitini, Brega da kuma Hreiqa.

Maido da ayyukan hakar man dai na kunshe ne a wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin bangaren Janar Haftar da mataimakin firai minister, Ahmed Maitiq da ke daya bangaren gwamnatin da ke hamayya a Tripoli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG