Masu ruwa da tsaki a harkar Man fetur a Najeriya, sun fara tofa albarkacin bakinsu game da garambawul din da shugaba Muhammadu Buhari yayi a ma’aikatan Man fetur na kasar.
Mataimakin shugaban kungiyar dillalan Man Fetur ta Najeriya, Abubakar Maigandi,yace canjin da aka samu yanzu yayi dai gani cewa ma’aikatar zata shiga taitayin ta domin tabbaci hakika idan aka yi ba daidai ba toh komai na iya faruwa, da fatan kuma za’a bi doka da oda.
Ya kuma umarci Gwamnati da ta dilasawa daffon daukar Man Fetur na NIPCO, da su saida masu Man akan farashi tunda sun riga su biyar kudadensu domin suma su sayarwa jama’a, akan farashi.
Masauna biranai masamman na Abuja da Lagos, na shiga gidajen Mai su cika tanki matukar suka ga damar ta samu domin gudun ko ta kwana na rashin tabbas din samuwar Man.