JOS, NIGERIA - Shugaban gamayyan darikun na Kirista kuma Shugaban darikar ECWA, Rev. Stephen Panya Baba, wanda ya jagoranci dukkan darikun zuwa kai tallafi wa 'yan gudun hijira da hare-haren 'yan bindiga ya rabasu da muhallansu a karamar hukumar Bokkos na jihar, ya bayyana takaicinsa kan yadda mutane fiye da dubu goma ke murkususu a sansani guda, tun fiye da wata daya, saboda rashin tsaro ya hana su komawa kauyukan su.
Sansanin na cikin garin Bokkos na dauke da mutane fiye da dubu goma sha tara, banda wadansu sansanoni goma sha biyu a wurare daban-daban a karamar hukumar ta Bokkos.
Wasu mata da Muryar Amurka ta zanta da su, sun shaida cewa babbar matsalarsu itace su samu abinci su kuma samu tsaro don komawa kauyukansu suyi noma.
Shugaban kungiyar mata Kirista ta CAN a jihar Filato, Madam Sarah Dalut ta gargadi matan ne kan su kare mutuncinsu.
Shima Shugaban kungiyar CAN a karamar hukumar Bokkos, Rev. Stephen Asugum ya ce suna bukatar kayan gine-gine don sake gina muhallansu.
Bayanai dai na nuni da cewa Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya amince da gina barikin soji a yankin Mbar na karamar hukumar Bokkos don tabbatar da tsaro a yankin.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:
Dandalin Mu Tattauna