Bayan sun kwashe sa'o'i da dama suna tattaunawa, al'ummomin Fulani da Tibabe da Jukunawa sun rabtaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen tashin-tashina tsakaninsu, lamarin da ya kaiga asarar rayuka da dukiya mai yawa.
Alhaji Mafindi Umar Danburam, shine shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar Taraba, ya bayyana yarjejeniyar da suka cimma. Yace sun sa hannu a takarda zasu zauna lafiya. Ya kira mabiya bayansu Fulani da Tibabe da Jukunawa, cewa sun yadda su zauna lafiya. Yace aiwatar da yarjejeniyar bashi da wuya idan gwamnati ta shigo kuma ta shirya.
Alhaji Mafindi yace yayin da suka kammala sa hannu akan yarjejeniyar, sun ji Jukunawa sun kai hari a Gwiwar Kogi inda suka jima mutane rauni suka kuma kona gidaje. Yace yana son suje har can Gwiwan Kogin su gaya masu cewa idan su Jukunawa suna cigaba da fada, zasu ga shugabanninsu dana Fulani, dana Tibabe da nasu sun ce a zauna lafiya. Suna son kowa ya zauna lafiya. "Duk wani mai korafi ya kawo a rubuce ma kwamiti da mukaddashin gwamnana jihar ya kafa a karkashin Bishop Linus su dubi maganar su gani wanene yake da damuwa. Ta yaya za'a warware damuwarsa."
Shi ma John Nunguwa, shugaban hadakar Tibaben jihar Taraba yace zasu hada kai wajen tabbatar da zaman lafiya. Yace idan Bafullatani ya shiga gonarka a zauna a shirya.
An sa hannu a yarjejeniyar a gaban manyan jami'an tsaro, da ma mukaddashin gwamnan jihar, Alhaji Garba Umar.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.