Shugaban Amurka Donald Trump ya tsige Shugaban Sashin ‘Yan sandan da ke ayyukan leken asiri na Secret Service, wanda shi ne sashin da ke kare shi, da iyalinsa, da kuma shugabannin Amurka na da.
Kafafen yada labaran Amurka da dama sun bayar da rahoto jiya Litini mai cewa, Shugaba Trump ya umurci mukaddashin Shugaban Ma’aikatan Fadar White House Mick Mulvaney, da ya sallami Shugaban Sashin ‘Yan sandan Ciki, Randolph Alles.
Shugaba Trump ne ya nada Alles, kuma ya kasance a kan wannan matsayin na tsawon shekaru biyu. Babu wani bayani ga jama’a kan dalilin sallamar shi.
“Ya yi aiki sosai a wannan sashin a tsawon shekaru biyu, kuma Shugaban kasa ya na mai cike da godiya gare shi saboda tsawon shekaru 40 da ya kwashe ya na bauta ma kasar. Nan gaba kadan zai bar ofis din.” Inji Mai magana da yawun Fadar White House Sarah Sanders.
Ta kara da cewa, Trump ya gabatar da sunan James Murray, wanda dadadden dan sandan ciki ne, a matsayin wanda zai zama sabon shugaban sashin, daga watan gobe.
Facebook Forum