Hukumomin Libya sun rufe filin jirgin sama daya tilo da ake amfani da shi a Tripoli, bayan wani harin da aka kai da jirgin sama jiya Litini
Daukan wannan mataki na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fafatawa kan iko da birnin na Tripoli tsakanin bangarorin mayaka biyu da ke gaba da juna.
Jami’an tsaro da ke Filin jirgin saman Matiga da ke gabashin babban birnin kasar ta Libya, sun ce zuwa yanzu dai babu wani sashi da ya dau alhakin kai harin, wanda ya bararraka hanyar da jirage ke gudu a kai amma bai raunata kowa ba.
Dakarun da ke biyayya ga kwamandan soji, Janar-Khalifa Haftar, sun ci gaba da dannawa da niyyar kwace babban birnin kasar.
Firaministan Libya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, Fayez Sarraj, ya kira matakin na Janar Haftar yunkurin juyin mulki.
Da alamar da Haftar da dakarunsa sun kafu sosai a bayan garin Tripoli, amma Sarraj ya ce a shirye sojojin kasar su ke su tinkare su.
Facebook Forum