Firai ministan kasar Lebanon ya sanar da yammacin jiya Litinin cewa gwamnatin sa ta yi murabus, bayan gagarumar fashewa a tashar jirgin ruwa a birnin Beirut da kuma zanga zangar da ta biyo baya.
"Muna so mu bada kofar ceto kasar, taimakon da ‘yan Lebanon zasu bada gudunmuwa wurin nasarar sa", inji Firai Minista Hassan Diab, a jawabin sa na telebijin. Ya ce "a dan haka ina sanar daku murabus din wannan gwamnati. Allah Ya kare kasar Lebanon."
Ya dora alhakin matsalolin da kasar ke fuskanta kan ‘yan siyasa wadanda suka yi mulkin kasar tun bayan kammala yakin basasa na kusan shekaru 30. Ya ce sun yi wa tattalin arziki da siyasar kasar barna kana suka janyo bala’in na makon da ya gabata kuma ya yi kira ga yin lissafi.
Daga yanzu gwamnatin Diab zata kasance ta riko har sai an gudanar da sabon zabe. Sai dai bai fadi lokacin yin zaben ba, amma a baya ya ce zai fitar da dokar da zata sa a gudanar fa zabe da wuri.
Facebook Forum