Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zaman Makoki a Lebanon


Hayakin da ya tashi bayan fashewar
Hayakin da ya tashi bayan fashewar

Firai Minista Hassan Diab ya ayyana Laraba a matsayin ranar makoki a Lebanon, bayan da aka samu wata fashewa da ta girgiza yankin tashar jirgin ruwar da ke Beirut babban birnin kasar.  

Wata sanarwar da kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross fitar, ta ce mutum sama da 100 sun rasa rayukansu kana kimanin wasu 4000 suka jikkata.

Jami’ai sun ce ana fargabar alkaluman wadanda abin ya rutsa da su zai karu yayin da ake ci gaba da laluben baraguzan gidajen da suka rushe, kuma mutane suna ci gaba da neman ‘yan uwansu da abokan arziki.

Yadda fashewar ta hallaka gidaje
Yadda fashewar ta hallaka gidaje

Har yanzu ba a tabbatar da takaimaiman abin da ya yi haifar da fashewar da ta auku jiya Talata ba, sai dai jami’an Lebanon sun karkata hankalinsu akan abin da suka ce tulin sinadaran ammonium nitrate ne da aka ajiye a dakin adana kayayyaki da ke tashar jirgin har na tsawon shekara 6 da suka gabata.

Fashewar ta auku ne da yammacin, abin da ya yi sanadiyyar turnukewar hayaki a sararin samaniyya, kana girgizar ta tarwatsa kofofi da tagogi a tashar, tare da hantsila motoci da barnata gine-ginen da ke yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG