Ayyukan na gudana ne yayin da ake ci gaba da jimamin wadanda suka mutu a wata gagarumar fashewa a Beirut mai tashar jiragen ruwa.
A yau Alhamis ma’aikatar lafiyar kasar ta ce adadin wadanda suka mutu ya kai 137 kana wasu mutum 5,000 sun jikkata sanadiyyar fashewar- akwai kuma fargabar adadin zai karu a nan gaba.
Majalisar zartarwar kasar ta Lebanon ta ayyana har na tsawon mako biyu, inda ta umurci dakarun kasar da su yi daurin talala ga duk wanda ke da hannu a wannan fashewa, wacce ta auku a wani dakin tara kayayyaki da ke tashar jiragen ruwan, inda a nan ne lamarin ya faru.
A gefe guda kuma hukumomi na ci gaba da kokarin gano abin da ya haifar da fashewar inda shugabannin kasar ke tsammanin wasu tilin sinadaran ammonium nitrates ne da aka ajiye har na tsawon shekara shida a dakin adana kayayyakin, suka haifar da fashewar.
Shugaba Michel Aoun, ya sha alwashin cewa duk wadanda ke da hannu a wannan hadari za su fuskanci “tsattsauran hukunci.”
Facebook Forum