Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Duniya Za Su Tallafawa Lebanon


A jiya Lahadi Shugabannin kasashen duniya suka amince za su samar da gagarumin tallafi ga kasar Lebanon don taimaka mata wajen farfadowa daga babbar fashewar da ta faru a birnin Beirut a makon da ya gabata amma basu fadi yawan kudin da za su tura wa kasar ba.

Shugabannin, da suka gana ta bidiyo a yanar gizo bayan da shugaban Faranasa Emmanuel Macron ya kira taron, sun ce taimakon zai kasance akan lokaci, kuma isasshe don bukatun jama’ar Lebanon, kuma kai tsaye za a tura wa al’ummar kasar, yadda ya kamata kuma ta yadda kowa zai san yadda aka yi rabon.

Shugabannin manyan kasashen sun jaddada muhimmancin adalci da bayyana yadda aka raba tallafin agajin, saboda nuna shakkar tura wa gwamnatin tallafin, da ‘yan Lebanon da yawa ke gani tana tattare da ayukan rashawa kuma ana bayyana damuwa game da karfin da Iran ke da shi a kungiyar Hezbollah ta ‘yan shi’a

Macron, wanda ya kai ziyara Beirut ranar Alhamis din da ta gabata, ya fada a jawabinsa na bude taron da aka yi ta bidiyo cewa kasashen da zasu ba da tallafin na bukatar kawar da banbance-bambancensu don taimaka wa jama’ar Lebanon kuma MDD ce za ta shirya yadda za a raba tallafin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG