Matatar man Dangote tace ta rage farashin litar fetur dinta zuwa N899.50k domin saukakawa ‘yan Najeriya gabanin lokacin hutun bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.
A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun matatar Anthony Chiejina yace an tsara rage farashin ne domin saukaka farashin sufuri a lokacin bukukuwan.
A watan Nuwamban da ya gabata matatar mai zaman kanta ta rage litar fetur dinta zuwa N970.
“Domin rage farashin sufuri a wannan lokacin hutu, matatar Dangote na gabatar da rangwame a kan fetur din da take tacewa. Daga yau, za a rika samun litar manmu a kan N899.50 a sashen lodin manyan motocinmu ko kuma SPM.”
Dandalin Mu Tattauna