WASHINGTON, D. C. - An bayyana hakan ne a ranar Lahadin a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Ministan ma’adanai da ci gaban kasa wanda shine Shugaban kwamitin Ministoci, Dr. Oladele Alake.
A cewarsa, gwamnatin ta fahimci cewa, bisa al’ada, ‘yan Najeriya sun saba tafiya zuwa garuruwansu a karshen shekara, suna kuma hasashen cewa, halin matsi da ake fama da shi, da kuma karin kudin sufurida ake dangantawa da tsadar sufurin a karshen shekara na iya kawo cikas ga ‘yan kasa da dama.
Ya yi nuni da cewa, shirin sufuri na lokacin hutun Kirsimeti da karshen shekara zai cirewa dimbin ‘yan Najeriya kitse a wuta.
A ranar 19 ga watan Disamba, 2023, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da wani sabon shirin bayar da agajin sufuri wanda zai samar da sufuri kyauta a kan hanyoyin hukumar jiragen kasa ta Najeriya, NRC da kuma tallafin kashi 50 na kudin sufurin fasinjojin da ke tafiya kan tituna 28 da motocin bas a karkashin inuwar kungiyar Masu Bus-bus na Najeriya, ALBON
Dandalin Mu Tattauna