Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Sojojin Najeriya a Boko Haram - inji Sojan Najeriya - Kashi na Farko


Wani mutum da yace shi sojan Najariya ne daga Kwanduga a jihar Borno, ya fadi irin abubuwan dake wakana a bayan fage, dangane da yaki da kungiyar tayar da kayar baya da aka fi sani da Boko Haram, a hirar da yayi da Aliyu Mustaphan Sokoto na sashen Hausa.

Soja: Ni soja ne amma gaskiya bazan iya kiran sunana ba saboda sha’anin sharrin aikin mu na sojan Najeriya.

Aliyu Mustaphan Sokoto: Me kake so mu sani?

Soja: To tsakani da Allah abunda nake so in fada ma, ina so in fada ma duniya ne, sojan Najeriya sun dauke mu sunzo sun tara mu a Kwanduga, suna kaiwa suna komowa ana kashe mu daya bayan daya. Don babu dalilin da zai sa Kanal yazo ya samu Laftanal Kanal namu daga Kwanduga, ya debemu zuwa Bama yace mu shiga, bai fada mana ga inda zamu je ba. Sai da muka ankara, muka samu kanmu gamu ga Sanbisa. Sai da ya tura mu gaba, ya raba mana launin Kaki biyu, mu ya tura mu gaba da kalarmu na Kamo, shi kuma sojojinsa masu green inifom. Sai da ya bari mu isa har bakin daga, shi da tankokin yakin gaba daya, sai yace wa mutanensa su koma. Ya ja mutanensa baki daya suka koma da baya, suka barmu, mu kadai kawai sojojin kwanduga muka je muka shiga tsakiyar mutanennan. Sai da suka koma, ya ja tankokin yakin gaba daya ya koma sai yara kawai kanana aka bari ana ta kashe mu kamar ruwa. Saboda me? Shi shekara biyar yayi yana nan bashi da zuciyar yaje y agama wannan abun, ana nan ana cin zalin “innocent soul”. Mu kuma mun zo da zuciya daya, mun zo mu gama wannan aikin, amma yana cewa wai tunda muke zuwa kullum, muna cigaba, muna yi dasu, ba’a taba samun wanda ya rasa ransa ba, yazo ya debe mu ya shigo da mu ta can. Ya za’a yi ma ace sansanin Boko Haram, bai fi kilomita tsakanin sansanin Bama ba da inda suke, sannan su basu taba yin komai akai ba? Abun mamaki ma idan baka sani ba, da muka je ma, wadanda muke fada da su, sai muka samu a cikinsu ma akwai sojojin haya, wadanda sojojin Najeriya ne, wadanda su suka koyar damu a Kwantagora. An je an yo hayarsu an kawo su suna wannan aiki. A cikinsu akwai wadanda bazan iya kiran sunayensu ba, amma akwai sojoji wadanda mun sansu, malaman mu wadanda su suka koyar damu yaki da ta’addanci, kuma muka gansu a ciki. Sune masu harbin yaranmu an dauko su.

Aliyu Mustaphan Sokoto: Su wadannan sojojin wa suke yaka? Ku suke yaka ko ‘yan Boko Haram suke yaka?

Soja: Abun mamaki su raka mu kawai sukayi, wadanda suka zo daga Bama, 202, da suka raka mu, da muka gama shiga, sai su suka koma da baya, da su da tankunan yaki duka sai suka koma, wai mu kullum muna fada ba’a taba samun wanda ya rasa ransa ba, so yanzu sun kaimu kennan mu kennan mu samu asarar rayuka. Mu da bindigar AK 47 mun je muna fada da mutum mai bindigar AA, BMG, LMG… Ya za’a yi mutum mai AK yayi fada da mai LMG? Don Allah Oga zaka yarda? Mai AK 47 bai isa yaje yayi fada da mai MG bama, balle yaje ya tunkari mai AA.

Aliyu Mustaphan Sokoto: Wato maganar da akeyi na cewa sun fi ku (Sojoji) makaman kirki, dai-dai kennan.

Soja: Tsakani da Allah, ba karya, Najeriya Army tana da makamai amma a bamu, an ki. An yaudare mu tun daga Kwantagora aka kawo mana LMG, aka bamu muka gwada, aka horas da mu da shi, amma da muka zo nan, har yau banda karya, babu abinda Najeriya Army take mana. To me take yi mana? Karya kawai, ance za’a bamu LM, za’a yi me, amma kawai sai suyi ta bada umarni ‘move! move!! move!!!’. An kawo mana wani kwamanda yanzu haka yana kwance ana kara masa ruwa. Ya gagara yaci abinci, saboda ya san an kaishi a kashe shine.


Yau kusan kwanaki uku kennan Sashen Hausa yake neman hukumomin sojojin Najeriya a ciki harda yawan kiran babban sakataren ma’aikatar tsaron Najeriya, Alhaji Aliyu Noma domin mu basu damar mayar da martani ga wadannan kalamai amma bamu samu ji daga wajensu ba.

Sannu ahankali, zamu kawo muku ragowar wannan hira a kwanaki masu zuwa.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG