Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Zata Binciki Mutanen Da Suka Kaucewa Biyan Haraji


Shugaban Faransa Francois Hollande, ya ce gwamnatinsa za ta kaddamar da bincike kan wadanda suka kaucewa biyan kudaden haraji, ta hanyar boye kudadensu a bankunan ketare, kamar yadda wasu takardu da aka kwarmata masu taken “The Panama Papers” suka nuna.

“Wannan bayani wanda aka fitar, ya tabbatar da cewa za a iya yaki da masu gujewa biyan haraji, kuma dukkanin bayanan da aka fitar, za su kai ga hukuma ta binciki lamarin, a kuma tuhumi wadanda ake zargi.”

Wata gamayyar ‘yan jaridu masu bincike da ke da mazauni a nan Washington ce, ta wallafa wasu daga cikin sakamakon binciken da ta gudanar kan asusun wasu masu kudi da fitattun mutane da kuma wasu masu madafan ikon da ke boye kudadensu a kasashen waje.

Takardun dai sun bayyana yadda wasu ‘yan siyasa 140 da wasu jami’an gwamnati a duniya, ciki har da firai ministan Iceland David Gunnnlaugsson da shugaban Ukraine Petro Poroshenko da kuma na Argentina Mauricio Marci su ka boye kudadensu a bankunan kasashen waje domin gujewa biyan haraji.

XS
SM
MD
LG