China na kelen assiran Amurka ta hanyoyin yanar gizo, abinda ya janyo satar bayanan ma’aikatan gwamnatin Amurka, inda zata saka takunkumi kan mutane ko kamfunnan da suka amfana da bayanan sirrin da aka sata.
Jaridar ta Ambato wasu kusoshin gwamnatin Amurka da ba’a bayyana sunayensu sa ban a cewa, har yanzu Amurka bata yanke shawara ba ko zata saka takunkumi ba, amma nan bada dadewa zata yanke shawara kan batun.
Tun ran Daya ga watan Afrilu ne shugaba Obama ya rattaba hannu kan wata doka ta ta umurci baitulmalin Amurka hade da opishin atone-janar na kasar da sakataren harkokin waje, cewa su dakatar da kudade da kaddarorin duk wanda aka samu da laifin leken assiran gwamnatin Amurka da satar bayanai ko cin moriyar su.
An jima ana zargin Kasar China da laifin koarin neman satar assiran kamfanonin Amurka da ma gwamnati. A watan Mayu Amurka ta zargi wasu manyan jami’an Sojoji da satar bayanan kasuwanci kan wasu kamfanonin Amurka. Amma China ta karyata zargin.