Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sojan Nijar Ta Daure Wasu Ministocin Gwamnatin Bazoum


Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Hukumomin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar sun tisa keyar wasu mukarraban hambararriyar Gwamnatin kasar zuwa gidajen yari daban-daban a jihohin Tilabery da Yamai, yayin da aka ba da sanarwar kafa wata sabuwar hukumar yaki da cin hanci da farautar mahandama dukiyar kasa.

NIAMEY, NIGER - Wadanda Gwamnatin mulkin sojan na Nijar ta tura gidan kaso sun hada da Ministan cikin gidan hambararriyar Gwamnati Hama Souley Adamou, wanda a yammacin Laraba 20 ga watan Satumba aka kai shi kurkukun Kollo da ke tazarar kilomita 25 da birnin Yamai.

Sai Ministan man fetur Mahaman Sani Mahamadou dan tsohon shugaban kasa Mahamadou Issouhou wanda shi kuma ya shafe darensa na farko a gidan yarin Filingue da ke tazarar kilomita 180 daga birnin Yamai.

Haka kuma an tisa keyar tsohon Ministan kudi Ahmed Djidoud zuwa kurkukun Say, yayin da shi kuma Shugaban jam’iyar PNDS Foumakoye Gado aka ajiye a gidan kason Yamai.

Rahotanni na cewa matakin ya kuma rutsa da wasu jami’an na daban wadanda kawo yanzu babu karin haske game da sunayensu, lamarin da wani mai fafutuka ta yanar gizo, Bana Ibrahim ke ganin ya yi daidai.

A daidai lokacin da wannan al’amari na kulle jami’an tsohuwar Gwamnati a gidajen yari ke wakana, majalisar mulkin soji ta CNSP ta hanyar kakakinta Kanar Manjo Abdourahamane Amadou, ta ba da sanarwar kafa wata sabuwar hukumar yaki da cin hanci da farautar mahandama da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa COLDEF a takaice.

Hukumar na da cikakken iko da ‘yancin gudanar da aikin tsaftace harkokin kudi da tattalin arziki.

A ra’ayin wani matashi dan siyasa Habila Rabiou, akwai yiwuwar sabuwar hukumar ta yi tasiri wajen kwato dukiyar jama’a daga hannun mahandama.

To sai dai Shugaban kungiyar yaki da cin hanci ta ANLC reshen Transaparency International, Malam Maman Wada na cewa karfafa hukumar HALCIA da kayan aiki shi ne hanya mafi a’ala don samar da sakamakon da ake fata a maimakon kafa wata sabuwar hukuma.

Yaki da cin hanci da farautar mahandama na daga cikin bukatu na gaba-gaba da masu goyon bayan sojojin CNSP suka sha bayyana fatan ganin an maida hankali akansu don ganin an hukunta ‘yan siyasa da ‘yan kwangilar da ake zargi da rub-da-ciki da dukiyar kasa musamman wadanda a baya suka kasance tamkar kadangaren bakin tulu ga gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG