Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yi barazana farkon wannan mako cewa, za a dorawa Iran mummunar takunkumin kudi da ba a taba ganin irinsa ba, idan bata sake halayenta ba, inda ya lissafo jerin bukatu 12 a kan sabuwar yarjejeniyar nukiliya.
Le Drian ya fadawa wani gidan rediyon kasar ta France Inter cewa, dora sabbin takunkumai ba zai karfafa tattaunawa ba, sai dai ma zai taimakawa ra'ayin rikau na Iran, yayin da kuma zai raunana shugaba Hassan Rouhani.
Yace wannan matsaya da Amurka ta dauka nada hadarin gaske ga yankin.
Bugu da kari a kan shirin nukiliyar Iran da ayyukanta a yankin, Pompeo ya lashi takobin maido da Amurkawa da aka yi garkuwa dasu a Iran.
Facebook Forum