Dadadden Shugaban Kamaru, Paul Biya, ya bayar da sanarwar cewa zai sake tsayawa takara na wani wa'adi, a wani yinkuri na tsawaita mulkin da ya yi tsawon shekaru 36 ya na yi.
Biya, dan shekaru 85 da haihuwa, ya fadi ta kafar twitter jiya Jumma'a cewa zai tsaya takara a zaben da za a yi a watan Oktoba. Ya ce zai tsaya takara ne don tabbatar da ganin cewa kasar ta Kamaru ta dada zama dunkulalliya, mai kwanciyar hankali da kuma cigaba.
Ya kara da gaya ma 'yan kasar ta Kamaru cewa, "A shirye na ke in amince da wannan kiraye-kirayen da ku ke ta yi babu kakkautawa."
Biya ya yi ta shugabantar Kamaru tun daga 1982 kuma idan ya zake cin zabe a karo na 7, zai shugabanci kasar har lokacin da ya zama dan shekaru fiye da 90 a duniya.
Facebook Forum