Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Famfuna Sun Bushe Yayin Wani Rashin Ruwa Da Ba Taba Gani Ba A Birnin Johannesburg


APTOPIX Johannesburg Rashi Ruwa
APTOPIX Johannesburg Rashi Ruwa

Makwanni biyu ke nan Tsholofelo Moloi yana cikin dubban 'yan Afirka ta Kudu da ke yin layi don samun ruwa yayin da babban birnin kasar, Johannesburg, ke fuskantar rugujewar tsarin kayan aikin ruwa da ba a taba gani ba.

WASHINGTON, D. C. - Mazauna birnin masu arziki da matalauta ba su taɓa ganin ƙarancin ruwa mai tsananin haka ba. Yayin da yanayin zafi ya ruguje magudanan ruwa, da durkushewar ababen more rayuwa bayan shekaru da yawa da rashin kula na cikin dalilai da suka jawo rashin ruwan.

Johannesburg
Johannesburg

Bacin ran jama'a wata alama ce mai hadari ga jam'iyyar National Congress mai mulkin kasar, wadda rike madafun iko cikin jin dadi tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a shekarun 1990 yanzu ke fuskantar kalubale mafi girma a zaben bana.

Moloi, mazaunin Soweto da ke wajen birnin Johannesburg, ba ta da tabbacin ita ko maƙwabta za su iya ci gaba da dauka wannan damuwa haka.

Su da sauran su a fadin cibiyar tattalin arzikin Afirka ta Kudu mai kimanin mutane miliyan 6 suna layi kowace rana don jiran motoci masu dakon ruwa na kananan hukumomi. Kafin manyan motocin su iso a ranar da ta gabata, Moloi don matsananciyar wahala sai da ta nemi ruwa daga wani gidan abinci da ke kusa.

Johannesburg
Johannesburg

Babu wani madadin. Ana sayar da kwalaben ruwa mai lita biyar (gallon 1.3) akan rand 25 ($1.30), wanda ya yi tsada ga yawancin mutane a kasar da sama da kashi 32% na al'ummar ba su da aikin yi.

Mazauna birnin Johannesburg da kewaye sun dade suna ganin karancin ruwa ba wai a duk fadin yankin ba a lokaci daya.

A karshen mako, hukumomin kula da ruwa a lardin Gauteng, wanda ya hada da Johannesburg da Pretoria, babban birnin kasar, sun shaidawa jami'ai daga garuruwan biyu cewa, rashin rage yawan amfani da ruwa na iya haifar da rugujewar tsarin ruwan gaba daya.

Wannan yana nufin tafki zai ragu ƙasa da ƙarfin kashi 10% kuma ana buƙatar a rufe don ya sake karuwa.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG