Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra’ila Sun Umarci Falasdinawa Su Fice Daga Arewacin Zirin Gaza


Wasu Falasdinawa yayin da suke nemn mafaka a yankin Zirin Gaza
Wasu Falasdinawa yayin da suke nemn mafaka a yankin Zirin Gaza

Yankin na Gaza na karkashin kawanyar Isra’ila, wani mataki da Isra'ilan ta dauka a matsayin martanin mummunan harin da Hamas ta kai wa Isra’ilan a ranar Asabar din da ta gabata, wanda ya halaka daruruwan fararen hula.

Dakarun Tsaron Isra’ila (IDF) sun nemi fararen hula a da ke zaune a yankin arewacin Zirin Gaza da su fice daga yankin domin tsira da ransu.

Cikin wata sanarwa da dakarun suka fitar a shafin X, Kakakinsu Jonathan Conricus, ya bukaci fararen hular da su nausa zuwa Wadi Gaza da ke kudancin Zirin.

“Za ku dawo birnin na Gaza idan muka sanar da hakan. Kada wani ya tunkari shingen tsaro na Isra’il.” Conricus ya ce.

Wannann sanarwa ta biyo bayan wata sanarwa da dakarun na Isra’ila suka fitar wacce ke kira ga al’umar Falasdinawa da yawanta ya kai miliyan 1.1 su koma kudanci cikin sa’a 24.

“Majalisar Dinkin Duniya na ganin wannan abu ne da zai yi wuyar faruwa ba tare da an samu tangarda ba.” Mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya ce.

“Majalisar Dinkin Duniya na neman a janye wannan sanarwa idan har ta tabbata hakan ne, domin kaucewa kara dagula al’amura.” Majalisar Dinkin Duniya ta ce.

Yankin na Gaza na karkashin kawanyar Isra’ila, wani mataki da Isra'ilan ta dauka a matsayin martanin mummunan harin da Hamas ta kai wa Isra’ilan a ranar Asabar din da ta gabata, wanda ya halaka daruruwan fararen hula.

Falasdiwan da ke zaune a yankin na zaune babu wutar lantarki, ruwa da man fetur.

Rahotanni na nuni da cewa, Isra'ilan na shirin tura dakarunta cikin yankin na Gaza ne a kafa.

Kungiyar Hamas ta yi ikirarin kama Yahudawa sama da 100 cikin har da sojojin kasar.

Sama da mutum 2,300 suka mutu a bangaren Isra'ilan da Gaza tun bayan barkewar rikicin.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG