Fakewa da addini wajen kai hare-haren ta’addanci ya sanya shugabannin Musulmai da Krista a Najeriya nesanta addinan daga wannan ‘dabi’a.
Hari irin na makon jiya da aka kai kan masallaci a Mubi, inda fiye da mutane 50 suka rasa rayukansu, da wasu hare-hare dake faruwa a Arewa maso Gabashin Najeriya da kuma fitinar kabilanci da kan rikide hakan ya sa shahararren malamin Islama Sheik Yakubu Musa Hassan Katsina, nuna matukar damuwa.
Inda Sheik Yakubu ya ce, “a inda ma ake jihadin, annabin rahama da duk wani jagora ya kan sanar da kwamandoji cewa banda kashe yara kanana, banda kashe mata, banda kashe masu ibada.” Ya ci gaba da cewa wadanda ake fada dasu sune kadai abokan fada.
Haka kuma malamin yayi kira ga jami’an tsaron da suke yaki da ta’addanci a kasar da su ‘dauki hikimar biyan lada da alkawarin boye sirrin duk wani da ya fito ya tona asirin mutanen dake kokarin zubar da jinin mutane a wajen ibada da sauran wurare.
Shima shahararren mai bishara Pasto Buru, ya ce a ganinsa idan anga mai fada da addini jahili ne da aka saka shi a hanyar ta’addanci don biyawa wasu mutane bukatunsu.
Pasto Buru, ya ce ana fakewa da guzuma ana harbin karsan ne wajen alakanta wasu laifuka da aka aikatawa da sunan addini, wanda hakan ba adalci bane domin babu addinin da ya koyar da tashin hankali.
Najeriya ta sha fuskantar fitina ta hanyar shiga rigar addini, kabilanci ko bangarenci, da kan haddasa asarar rayuka musammanma na talakawa.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum