Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Zata Baiwa Jihohi Naira Miliyon Dari Takwas


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Majlisar kula da tsara tattalin arzikin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ta gudanar da taro, inda ta amince da sake baiwa jihohin kasar rancen Naira miliyon dari takwas don biyan albashin ma’aikata.

Taron ya tattauna abubuwa da dama da suke yiwa tattalin arzikin Najeriya tarnaki da kuma hanyoyin da za a bi a magancesu. Batun yanda Najeriya zata rage dogaro da man fetir yana cikin muhimman batutuwa da taro ya tattauna a kai.

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Abubakar Bagudu ya yiwa wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka karin haske a kan batutuwan da taron ya tattauna akai. Ya ce taron ya tattauna a kan batun karban haraji daga masu hannu da shuni wadanda suke kin bayyana kadarorinsu ga hukumomi.

Duk da cewar wasu jihohi sun gaza biyan albashin ma’aiktansu da kudaden yan fansho bayan kudade da gwamnatin tarayya ta basu, wannan taro ya kuma amince ba jihohin karin wasu kudade don biyan albashi da sauran wasu muhimman bukatu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG