Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC ta yi Farin Ciki da Ficewar Atiku Abubakar Daga Cikinta


Shugaba Buhari da Atiku
Shugaba Buhari da Atiku

Ficewar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar daga jami’iyara APC mai mulkin Najeriya ta haifara da mahawara musamman tsakanin ita jami’iya mai mulki da babban jami’iyar adawa ta PDP.

Yayin ‘ya’yan PDP ke marhabi da sanarwar ficewar Atiku Abubakar daga APC, ita kuwa APC cewa take yi Allah raka taki gona.

Ya yin da ya isa jiharsa ta haifuwa ta Adamawa bayan sanarwar ficewarsa daga jami’iyarsa ta APC, Atiku ABauakar ya samu gagarumin tarbo daga yan jami’iyar adawa ta PDP a jihar, duk da cewar bai bayyana jama’iyar da yake niyar komawa ba.

Shugaban jami’iyar PDP a jihar Adamawa Barista Shehu, yace suna matukar farin ciki da wannan shawara da tsohon mataimakin shugaban kasar ya dauka saboda sun dade suna zawarcinsa tun bai yi tunani daukar wannan shawarar ba.

Kawo yanzu dai Atiku Abubakar bai fitar da wata sanarwa a hukumance a kan jami’iyar da zai koma ba, amma dai tsohuwar jami’iyar ta PDP ta fara kamun kafa da ya dawo tsohuwar gidansa da ya gina da dunkiyarsa da basirarsa.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG