Masu ruwa da tsaki kan lamuran yada labaru a Kano da suka kalli fefan bidiyon da Muryar Amurka ta shirya irinsa na farko kan yadda ta kasance dangane da tarzomar boko haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya, sunce baya ga Hausa akwai bukatar a fassara faifan zuwa sauran manyan harsunan Najeriya wato Yarbanci da kuma Igbo.
Shirin faifan bidiyon na Muryar Amurka wadda aka kwashe kimanin shekaru 2 ana shiryawa, ya nuna jajircewa cikin yanayin tausayi da mata yara da sauran wadanda wannan tarzoma ta rutsa dasu suka nuna. Baya ga karfafa gwiwar masu ruwa da tsaki su kara kaimi wajen kawo karshen tarzomar da kuma samar da kyakkyawar makoma ga yara da matan da fitinar ta galabaitawa rayuwa.
Wadansu da suka kalli bidiyon sun yi tambayoyi tare kuma da bada shawarwari bayan shafe tsawon sa’a guda ana kallon fefan bidiyon a ma’aikatar yada labarun Kano.
Malam Aliyu Mustafan Sokoto babban Editan Sashin Hausa Muryar ya amsa tambayoyi tare da yin karin haske kan silman.
La’akari da alfanun sakonnin dake cikin wannan faifan bidiyo, yasa ma’aikatar labarun Kano ta sha alwashin yada su a tsakanin daliban makaran jihar, kamar yadda daraktan wayar da kan jama’a Abdullahi Abubakar shanono ya bayyana. Shima a nasa jawabin, babban sakatare a ma’aikatar labarun Malam Abba Yakubu ya yaba da hangen nesan Muryar Amurka ta wannan fuska.
Shugabanni da jami’an kafofin labaru da sauran masu ruwa da tsaki ne suka halarci wurin nuna faifan bidiyon da aka yiwa lakabi Tattaki daga bakar akida.
Daga Kano ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari
Facebook Forum