Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lokaci Ya Yi Da Za A Ba Igbo Mulkin Najeriya - Ngige


Chris Ngige.
Chris Ngige.

Ministan kwadago da ayyuka kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Sanata Chris Ngigi, ya mara baya ga kiraye-kirayen da yan kabilar Igbo ke yi na mayar da ragamar shugabancin kasar zuwa shiyarsu ya na mai cewa, hakan zai taimaka wajen warware zargin rashin damawa da su.

Sanata Chris Ngige dai ya bayyana hakan ne a yayin amsa tambayoyi a wani shiri mai taken 'News Night a gidan talabijan na Channels, inda ya ce, ‘yan kabilar Igbo sun dade suna fafutukar ganin ragamar shugabancin ya koma shiyar su lamarin da ya kai ga rarrabuwar kawuna tsakanin al’umman shiyoyin kasar mai mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika.

A cewar Ngige, lokaci ya yi da za a mara baya ga wadanda ke kiraye-kirayen a mika ragamar mulki ga yan kabilar igbo a zaben shekarar 2023 mai zuwa inda ya yi imanin cewa, idan mulki ya koma kudu, za a magance rikice-rikicen da ke afkuwa a kudu maso gabas da kuma yadda yan shiyyar ke ganin an maida su saniyar ware musamman idan kujera mafi mahimmanci ta farko ta kasance da jagorancin dan kabilar Igbo.

‘Yan kabilar Igbo sun dade suna kai ruwa rana kan batun cewa, an maida yan yankin saniyar ware, ba a ganin darajarsu a shigo da su a dama da su duk da cewa ba zai iya tantance ko yadda su ke ji na da alaka da farfaganda ne ko akasin haka inda Chris Ngige ya ce, ya amince 100 bisa 100 da fafutukar ‘yan kabilarsa ta Igbo.

Karin bayani akan: Chris Ngige, Igbo, Channels, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Sai dai, kundin tsarin mulkin kasar bai bada wannan dama ba in ji shi kuma ya ce kullum yana da imanin cewa, kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1995 da marigayi Janar Sani Abacha ya gabatar na tsarin mulkin karba-karba zuwa shiyyoyi shida na Najeriya, mai wa’adin shekara biyar a wa’adi daya kacal domin ya warware duk radadin da aka ji sakamakon yakin basasa, da na zaben 12 ga watan Yuni zam taimaka matuka ga yanayim da kasar ke ciki.

A wani bangare kuwa, Chris Ngige ya ja hankali ga yan kasar da kada su kure shugaba Muhammadu Buhari don hakurinsa ya na mai cewa, ba wani shugaba da ya shanye duk sukar da aka yi masa kamar Buhari.

Daga karshe, Chris Ngige ya jadada kokarin gwamnatin tarayya na cika alkawuran da ta dauka a fannoni da dama, inda ya yi kira ga masu sukar gwamnati su ruka adalci.

‘Yan Najeriya da dama dai na ganin gwamnatin da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta ta gaza a fuskoki da dama inda su ke yi kira kusa kullum a kafafen sada zumunta da shugaban ya ajiye aiki don ba wa wani damar jarraba na sa kokari.

XS
SM
MD
LG